Posts

Showing posts from May, 2022

Sauya shekara ɗaya Buhari yayi bakwana da mulki

Image
Sauya shekara ɗaya Buhari ya yi bakwana da mulki Daga Jaridar Magarya Yau Lahadi 29 ga watan Mayun shekara 2023 saura kwanaki 365 shugaban ƙasar Najeriya Muhammadu Buhari ya yi bankwana da mulkin Najeriya. Tsawun shekara bakwai kenan jam'iyyar APC na mulkar al'ummar Najeriya kimanin miliyan ɗari biyu da ashirin sai dai jama'a na bayyana ra'ayoyinsu mabambanta game da kamun ludayin gwamnatin shugaba Buhari. Da me zaku iya tunawa da mulkin jam'iyyar APC a Najeriya?

Ɗan Bindiga Ya Fi Deligate Imani – Shehu Sani

Image
Ɗan Bindiga Ya Fi Deligate Imani – Shehu Sani     Daga Ibrahim Ammani Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya ce babu maraban ƴan bindiga da ‘Deliget’ a siyasan Najeriya. Shehu Sani ya bayyana cewa yadda mahara ke karɓar kuɗi a hannun waɗanda suka yi garkuwa haka suma ‘Deliget’ ke ƙarɓar irin wannan kuɗade a hannun mutane da sunan wai za su zaɓe su. "Na shiga siyasa ne domin a gyara tsarin tare da tsaftace shi ta yadda za a rika zaɓen nagartattun mutane waɗanda suka cancanta ta hanyar yin zaɓen mai aminci da nagarta tun daga zaɓen ƴan takara zuwa zaɓen shugabanni. "Ni fa a ganina ban faɗi zaben fidda gwani ba, ban yi nasara ne a kasuwanci siye da siyarwar ɗan takara ba ta hanyar wanda yafi zabga kuɗi ya kwashi dami. "Bai kamata ace wai ta irin wannan hanya ce za a riƙa zaɓen waɗanda za su shugabanci jama’a a ƙasar nan ba, saboda maimakon a zaɓi nagari mai dammai a aljihu ne za a baiwa mulki ko mai lalacewar sa kuwa. Hakan bai dace ba. "Gaba ɗaya t...

Yau ce Ranar Yaƙi Da Cutar Yoyon Fitsari

Image
Yau ce Ranar Yaƙi Da Cutar Yoyon Fitsari      Daga Jaridar Magarya Ranar 23 ga watan Mayun kowace shekara wasu Kungiyoyin da ke aikin jin ƙai sun ɗauki matakin magance matsalar tsakanin mata musamman waɗanɗa ke fama da matsalolin tsaro. Yayinda ake gudanar da bikin ranar yaki da cutar yoyon Fftsari da nufin kawo ƙarshen ta a cikin al’umma wasu ƙungiyoyin da ke aikin jin ƙai sun ɗauki matakin magance matsalar a tsakanin mata. Taken bikin na bana shi ne ƴancin Mata ‘Ƴan bani Adama ne a kawo ƙarshen cutar Yoyon Fitsari.”  Matsalar Yoyin fitsari ta na zama ruwan dare gama duniya a Najeriya inda ake samun ƙaruwar matsalar cutar ta yoyon fitsari inda ta shafi rayuwar dubun dubatar Mata.  Baki ya zo daya tsakanin Masana kiwon lafiya da masharhanta har da masu yaki da wannan matsalar inda su ke alaƙanta ƙaruwar ta da jahilci da kuma matsalolin da ake samu lokacin haihuwa da ma Auren wuri da ake yiwa wasu ƴan Mata da ba su tasa ba. Dubun dubatar Mata sun shig...

Manchester City Ta Lashe Gasar Firimiyar Ingila

Image
Manchester City Ta Lashe Gasar Firimiyar Ingila     Daga Jaridar Magarya Gundogan da Jesus suna murnar jefa kwallo. Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City ta lashe kofin gasar Firimiyar Ingila ta bana bayan ta farke ƙwallaye biyu da Aston Villa ta zira mata a filin wasa na Etihad. Wannan shi ne dai karo na shida da ƙungiyar ta lashe gasar a tarihi. Ƙungiyar da Pep Guardiola ke jagoranta ta kare kakar ta bana da tazarar maki daya kacal tsakaninta da Liverpool, wadda ta doke Wolves 3-1 a wasan ƙarshen da aka fafata a Yammacin ranar Lahadi. Ƙwallo biyu da Ikay Gundogan ya ci da kuma wadda Rodri ya zira a cikin minti shida kacal su ne suka bai wa City nasara inda ta lashe wasan da 3-2. Villa ta shiga gaba a wasan tun farko ta hannun Matty Cash da Philippe Coutinho.

Karon Farko Cikin Shekara 11 AC Milan Ta Lashe Gasar Serie A

Image
Karon Farko Cikin Shekara 11 AC Milan Ta Lashe Gasar Serie A    Daga Jaridar Magarya Bayan shekaru 11 ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta AC Milan ta lashe gasar Serie A ta bana da maki 86. Nasarar Milan na zuwa ne bayan ta doke Sassuolo da ci 3-0 a wasan ranar ƙarshe na gasar Serie A da aka fafata a Yammacin ranar Lahadi. Milan dai ta lashe hasar ne ita kuma babbar abokiyar hamayyarta, Inter Milan ta kare a mataki na biyu da tazarar maki biyu tsakaninsu. Ƴan wasan na Stafano Pioli sun jinjina kofin duk da nasarar da Inter ta yi 3-0 kan Sampdoria. Olivier Giroud ne ya zira ƙwallo biyu a wasan kafin daga baya Frank Kessie ya zura ta uku duk a cikin minti 36 da fara wasan. Karo na 19 ke nan jimilla da Milan wadda ake yi wa laƙabi da Rossoneri ta lashe babbar gasar Italiya ta Serie A a tarihi.

Sojoji Sun Ragargaza Sansanonin ISWAP A Borno

Image
Sojoji Sun Ragargaza Sansanonin ISWAP A Borno Daga A A Ngulde, Maiduguri Sojojin runduna ta 198, sun gudanar da gagarumin aikin ne tare da hadin gwiwar dakarun haɗin gwiwa na ƙasa da ƙasa (MNJTF) dake yankin tankin Chadi, domin fatattakar ƴan ta’addan a ƙaramar Hukumar Kukawa dake arewacin Jihar Borno. Wani jami’in leƙen asiri, ya ce yankunan da sojojin suka kwace a hannun mayaƙan ISWAP su ne Kangarwa, Alagarno, Daban Masara, Kwatan Daban Masara, Grede, Makar, Daban Karfe, Bulawa, Daban Gajere, Kwatan Garba, Ali Sharafti da kuma Tamfalla (kasuwar kifi) daga hannun ƴan ta’addan. Majiyar ta shaida wa Zagazola Makama, ƙwararre kan yaki da tada kayar baya, kuma manazarcin harkokin tsaro a yan Tafkin Chadi, cewa an ƙashe wasu ƴan ta’addar da ba a tantance adadinsu ba a lokacin da sojojin suka kai farmaki maɓoyarsu kuma da yawa daga cikinsu suka gudu suka bar kayansu. Majiyar Jaridar Magarya sun bayyana cewa a ci gaba da kai hare-hare ta ƙasa da jiragen yaki a yankin...

Badaƙala; EFCC ta kama tsohon shugaban hukumar yankin Neja-Delta

Image
Badaƙala; EFCC ta kama tsohon shugaban hukumar yankin Neja-Delta   Daga A A Ngulde, Maiduguri   Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ya tsare tsohon shugaban hukumar yankin Neja-Delta Mista Nsima Ekere bisa zargin zamba da ƙuɗi naira biliya 47. Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) a ranar Larabar da ta gabata sun kama tsohon Manajan Darakta na Hukumar Raya Yankin Neja-Delta (NDDC) Nsima Ekere bisa zargin karkatar da kudade da suka kai Naira biliyan 47 ta hannun ƴan kwangilar hukumar da suka yi rajista.  Mai magana da yawun hukumar na NDDS Wilson Uwajaren ya tabbatar da hakan ne ga gidan talabijin na Channels.  Shi dai tsohon shugaban hukumar ta NDDC ya kasance dan takarar gwamnan jihar Akwa Ibom na jam’iyyar All Progressives Congress  (APC) a zaben 2019. Ya kuma sha kaye a zaɓen fidda gwani na gwamna a jam’iyyar PDP a hannun Gwamna Emmanuel Udom a shekarar 2015.  Nsima mai shekaru 56 d haihuwa ya kasance M...

Badaƙala: Ministar Kudi, ta kori Akanta-Janar na Najeriya.

Image
Badaƙala: Ministar Kudi, ta kori Akanta-Janar na Najeriya.   Daga Jaridar Magarya Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta kori Akanta-Janar na Najeriya, Ahmed Idris daga mukaminsa saboda zargin badakalar Naira biliyan 80. Matakin na zuwa ne kwana biyu bayan Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta cafke shi saboda zargin karkatar da kudaden. Wasikar ta ce, Biyo bayan korarka da EFCC ta yi, saboda zargin karkatar da kudaden da yawansu ya kai Naira biliyan 80, ina sanar da kai cewa an dakatar da kai daga mukaminka daga ranar 18 ga watan Mayun 2022, ba tare da biyanka kowanne kudi ba. “An dauki matakin ne don a samu damar aiwatar da cikakken bincike a kanka ba tare da katsa-landan ba, kamar yadda Dokokin Aikin Gwamnati suka tanadar. "A iya tsawon wannan lokacin, ana so ka kauracewa ofishinka kuma kada ka halarci kowane irin taro ko ofishin gwamnati, har sai an gayyace ka,” inji wasikar.

Taraba: Sabon Rikici Ya Kunno Kai A Jam’iyyar APC

Image
Taraba: Sabon Rikici Ya Kunno Kai A Jam’iyyar APC           BASHIR ADAMU, JALINGO Wani sabon rikici ya ɓarke a Jam’iyyar APC ta Jihar Taraba sakamakon sauya zaɓaɓɓun Shugabannin Ƙananan Hukumomi guda hufu. A ranar Asabar ne Jam’iyyar APC ta sake rantsar da wasu sabbin Shuwagabannin ƙananan hukumomin Ussa, Wukari, Ibi da Takum. Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Taraba, Ibrahim Tukur El-sudi ne ya jagoranci rantsarwan, inda wasu bayanai ke cewa yayi hakan ne bisa umurnin Uwar Jam’iyyar ta ƙasa da ta turo mishi da sunayen waɗannan sabbin Shugabanni guda huɗu. Inda yace waɗannan zaɓaɓɓun Shugabannin da aka sauya, su daina bayyana kansu a matsayin shugabannin Jam’iyyar domin tuni aka yi waje rot dasu, duk da cewa ba’a bayyana laifin da suka yi aka ciresu ba. Sai dai kuma a wani mataki na maida martani game da matakin na El-sudi, ƙungiyar ƴakin neman zaɓen Gwamnan Jihar Taraba na David Sabo Kente, sun shaidawa Shalkwatan Jam’iyyar APC na ƙasa da su gaggauta wannan yunƙu...

Ƴan Bindiga Sun Sace Matafiya A Hanyar Abuja

Image
Ƴan Bindiga Sun Sace Matafiya A Hanyar Abuja           Daga Jaridar Magarya Rahotannin daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa ƴan bindiga masu garkuwa da mutane sun sace matafiya da dama a hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Talata wani wanda ya shaida lamarin ya bayyana wa BBC cewa lamarin ya faru ne a garin Katari da misalin 4:30 na yammaci. Ya bayyana cewa akwai motoci da dama waɗanda suna ajiye a ɓangaren zuwa Kaduna da aka yi awon gaba da masu motocin. Ya kuma ce bayan faruwar lamarin jami’an tsaro masu ɗimbin yawa sun isa wurin domin kai ɗauki. Muryar Ƴanci ta ruwaito cewa dukkanin kokarin da aka yi na jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ya ci tura saboda baya ɗaukar waya.

Fashewar Tukunyar Gas: Hukumomin tsaro sun tabbatar da mutuwar mutum huɗu A Kano

Image
  Fashewar Tukunyar Gas: Hukumomin  tsaro sun tabbatar da mutuwar mutum huɗu  A Kano          Daga A A Ngulde, Maiduguri     Hukumomin tsaro a jihar Kano            sun   tabbatar da mutuwar mutum       huɗu bayan fashewar wani abu           da ake zargin tukunyar gas ce a         unguwar  Sabon Gari da ke Kano          a safiyar Talata.      Kwamishinan Ƴan Sandan Jihar           Kano, Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya       ce an gano gawarwakin mutum            huɗu sannan yace jami’an tsaro          na ƙoƙarin gano ko akwai sauran        jama'a a cikin ɓaraguzan ginin            da iftila’in na safiyar Talata ya...

Shugaban Ƙasar Nijar Ya Haramta Wa Ministoci Ƙarin Aure

Image
Shugaban Ƙasar Nijar Ya Haramta Wa Ministoci Ƙarin Aure    Daga A A Ngulde, Maiduguri Shugaban Ƙasar Jamhuriyar Nijar,  Bazoum Mohamed, ya haramta wa ministocinsa ƙarin aure. Shugaba Bazoum ya ce duk ministan da ke slda ɓuƙatar ƙarin aure to ya sauƙa daga muƙaminsa, a wani mataki da shugaban ya ce zai taimaka wajen rage yawan haihuwa barkatai a ƙasar. Ya ce ya shaida wa ministocina cewa ya haramta musu ƙarin aure, matuƙar suna cikin gwamnatinsa. “Idan akwai ministan da ke son yin ƙarin aure ba za mu hana shi ba, amma kuma wajibi ne ya sauƙa dama muƙamin Gwamnatin Tarayya,” inji Bazoum. Bazoum ya sanar da gargadin ne a wurin wani taron mata da aka gudanar a ranar 13 ga watan Mayu, domin bikin ranar Mata da ake ui shekara-shekara, inda mahalarta suka yi ta shewa suna yabawa da wannan matakin. Sai dai furucin shugaban sun tada jiniyar wuya a sassan Jamhuriyar Nijar, domin kuwa wani ɓangare ya caccaki shi a kan matakin da ya ɗauka na hana ƙarin aure. Da yake jawab...

Hukumar EFCC Ta Damke Akanta Sakamakon Harƙarlan Biliyan 80.

Image
Hukumar EFCC Ta Damke Akanta Sakamakon Harƙarlan Biliyan 80. Rahotannin daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta kama Akanta Janar na tarayya bisa zarginsa da almundahana ta naira biliyan 80. Hukumar ce ta bayyana haka a shafinta na Facebook inda ta ce ta kama shi a ranar Litinin 16 ga watan Mayun 2022. Hukumar na zargin Ahmed Idris da karkatar da kuɗin ta hanyar amfani da abokansa da iyalai da sauran hanyoyi. EFCC ta ce an yi amfani da kuɗin wurin gina rukunin gidaje a Kano da Abuja. Ta kama Idris ne bayan ya ƙi ƙarɓar gayyatar da EFCC ta rinƙa aika masa domin tuhumarsa kan zarge-zargen da ake yi masa, kamar yadda hukumar ta bayyana.

Rundunar Ƴan sandan Jihar Borno Ta Tarwatsa Nakiya A Sansanin Dalori

Image
Rundunar Ƴan sandan Jihar Borno Ta Tarwatsa Nakiya A Sansanin Daori Daga Adamu Aliyu Ngulde, Maiduguri Rundunar ƴan sandan jihar Borno tayi nasarar tarwatsa nakiya da wasu maƙiya zaman lafiya suka ɗana a sansanin ƴan gudun hijira na Dalori dake hanyar Maiduguri zuwa ƙaramar hukumar Bama. Wannan sansani na Dalori mai nisan kilomita goma daga birnin Maiduguri ya ƙunshi ƴan gudun hijira masu yawan gaske da samun mafaka tsawun shekaru sakamakon hare-haren mayaƙan Boko haram da ya raba su da muhallinsu. Ƙwamishinan ƴan sandan jihar Borno Abdu Umar ne ya bayyana hakan yayin da yake yiwa manema labarai ƙarin bayani kan nasarar da ayarin ƴan sanda masu kunce bama-bamai suka yi da safiyar ranar Litinin. Yace domin daƙile barazanar da wasu ɓata gari ke yi domin tada husuma a tsakanin al'umma, ƙwararrun sun garzaya wurin da sanyin safiyar ranar Litinin tare da yin bincike a yankin sun kuma samu sa'ar tarwatsa wa da kuma kwashe raguwar bama-baman da aka dasa domin k...

Buhari Ya Yi Tir Da Kisan Deborah A Sokoto

Image
Buhari Ya Yi Tir Da Kisan Deborah A Sokoto Daga Ibrahim Ammani, Kaduna Shugaban Ƙasa Buhari ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyayen ɗalibar kwalejin Shehu Shagari dake Sokoto wanda ajali ya iske ta bayan an zarge ta da yin kalaman ɓatanci ga Annabi SAW. Buhari ya ce doka ba ta ba wani damar yanke hukunci kai tsaye ba. komai na da hurumin sa. Idan an yi laifi sai kuma a bari waɗanɗa hukunci ke hannunsu su yanke shi ba kowa ya yi gaban kansa ba. A sakon da ya fitar wanda kakakin shugaban Garba Shehu ya saka wa hannu, Buhari ya yabawa wa gaggawar ɗaukar mataki da gwamnatin Sokoto ta ta yi a lokacin da abin ya auku. "Babu wanda yake da damar yanke hukunci ko ɗaukar doka a hannun sa a ƙasar nan. Tashin hankali ba zai haifar da ɗa nai ido ba.

Tsaro: An Yi Wa Arewa Zobe– Zakzaky

Image
Tsaro: An Yi Wa Arewa Zobe– Zakzaky Daga Ibrahim Ammani, Kaduna A sakon da ya fitar na murnar bikin sallah karama, Shugaban Ƙungiyar IMN (Shi’a) ta ƙasa Sheikh Ibrahim Yakubu El Zakzaky ya bayyana yadda maƙiya suka taso yankin Arewa Shugaban ƙungiyar ta ‘yan Shi’a ya bayyana wasu abubuwa guda uku waɗanda sune jigajigan ƙarfin arzikin Arewa kuma ake burin ruguza su. 1-Noma. wadda ita ce tushen arzikin mutanen yankin, yanzu ta gagara, an hana manoma aiki an ƙore su daga garuruwan su, wanda ya zauna za a kashe shi. 2-Kiwo. Makiyaya an kashe ana kwashe dabbobin su. 3-Kasuwanci. Sufurin kayayyaki ya zama haɗari, saboda ayyukan ƴan ta’adda a hanyoyi. Sai gobara a kasuwanni wadda ba ta lafiya bace a rasa mai ya haddasa ta. Ɗan kasuwa idan yabi hanya a sace shi a nemi kudin fansa, sai dai a kwashe jarin sa a fanso shi ya dawo ba abin juyawa. Su kuma manyan yankin ba wannan ne ya dame su ba, in dai za a ba mutum mukami shi kenan kawai.

Jonathan ya yi watsi da fom din takarar da aka saya masa

Image
Jonathan ya yi watsi da fom din takarar da aka saya masa  Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya nesanta kan sa daga wadanda suka ce sun saya masa fom domin tsayawa takarar shugaban kasar zaben da za a yi a shekara mai zuwa a karkashin Jam’iyyar APC mai mulki. Wata sanarwar da mai magana da yawun sa Okechukwu Eze ya rabawa manema labarai ta ce Jonathan bashi da wata masaniya game da saya masa takardar takarar kuma bashi da wata alaka da wadanda suka ce sun saya masa. Sanarwar ta bukaci 'yan Najeriya da su yi watsi da rahotanni cewar zai tsaya takara a Jam’iyyar APC duk da ya ke sun san cewa wasu daga cikin kiraye kirayen da ake wa tsohon shugaban na da matukar tasiri. Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a yayin mika mulki ga Muhammadu Buhari a 2015. Tun farko dai wata kungiyar ‘yan arewacin Najeriya da ake dangantawa da Fulani ce ta sanar da biyan Jam’iyyar APC naira miliyan 100 domin karbar fom din takarar zaben ...

Shehun Borno ya nada sabon Shettima Mallumbe

Image
Shehun Borno ya nada sabon Shettima Mallumbe Mukhtar Alkali, sabon Shettiman Ilimi na ƙarbar takardar nadin sa  Daga A A Ngulde, Maiduguri Mai martaba Shehun Borno Alhaji Dr. Abubakar Ibn Umar Garbai Al-amin El-kanemi ya amince da naɗin Malam Mukhtar Alkali a matsayin Shettima Mallumbe na Borno, daya daga cikin manyan masu riƙe da sarautar gargajiya a masarautar daular Kanem Borno.  Alhaji Grema Isa, (Grema Balbalbe) na Borno shi ne ya miƙa takardan naɗin a yayin hutun ƙarshen mako ga sabon mai riƙe da muƙamin. Da yake gabatar da takardar nadin ga Mukhtar Alkali, Alhaji Grema ya ce naɗin Mukhtar Alkali ya kasance bisa cancanta domin ya gaji mahaifinsa marigayi Shettima Alkali Habib wadda ya rasu a shekarar da ta gabata. Dimbin al'umma waɗanɗa zuri'ar Shettima Habib duk sun hallara tare da shaida miƙa takardan ga Mukhtar Alƙali.  Da yake jawabi a madadin iyalan gidan marigayi Shettima Habib, Alhaji Bakura Mallam Lawan ya bayyana farin ci...

Najeriya Na Buƙatar Megawat Dubu 100 Don Magance Matsalar Lantarki – Minista

Image
Najeriya Na Buƙatar Megawat Dubu 100 Don Magance Matsalar Lantarki – Minista Daga Adamu Aliyu Ngulde, Maiduguri Tsohon Ministan Wutar Lantarki, Farfesa Barth Nnaji, ya ce Najeriya na buƙatar megawat dubu 100 na wuta in har ta na buƙatar magance matsalar wutar lantarki a ƙasa nan. Nnaji ya bayyana hakan ne ranar Juma'a yayin ganawa da manema labarai a Enugu game da makomar wutar lantarki. Ya ce ƙasar nan na fama da matsaloli a ɓangaren samar wa, yaɗa wa da rarraba wutar lantarki a ƙasa nan. Ya ƙara da cewa wannan shi ne ya sanya zai yi wuya a samu isashshiyar wutar lantarki ga ƴan kasa.

Borno: Boko Haram Sun Kai Hari A Ƙauyen Kautikari

Image
 Borno: Boko Haram Sun Kai Hari A Kautikari Daga Adamu Aliyu Ngulde, Maiduguri Rahotanni daga ƙauyen Kautikari na ƙaramar hukumar Chibok dake kudancin jihar Borno na cewa wasu da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne sun kai haei da maraicin nan. Da yake jawabi ga wakilinmu na jihar Borno DPO na Ƴan sandan ƙaramar  hukumar Chibok ya tabbatar da faruwar lamarin. Inda yace "Dazu da yamma na samu labarin wasu mahara sun kai hari garin Kautikari kuma tuni jami'an ƴan sanda suka kai ɗaukin gaggawa sai dai har zuwa yanzun bamu san halin da ake ciki ba" Muna sa ran da safe zamu samu damar yin ƙarin kan abin da ya faru" inji shi.

Sakatare Janar na MDD ya ziyarci Maiduguri

Image
Sakatare Janar na MDD ya ziyarci Maiduguri  Daga Adamu Aliyu Ngulde, Maiduguri Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ziyarci birnin Maiduguri sannan ya gana da Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum da kuma nabban jami’in Majalisar Dinkin Duniya kana mai kula da ayyukan jin ƙai Mista Mathias Schmale a filin jirgin saman Maiduguri.  Hakazalika sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ziyarci Maiduguri babban birnin jihar Borno da yammacin yau a ci gaba da ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Najeriya. Wakilinmu Adamu Ngulde ya ruwaito mana cewa ana sa ran Mista Guterres zai tattauna da mai masaukin baƙi Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum da kuma tattauna da tuɓaɓɓun mayaƙan da suka miƙa wuya da waɗanɗa rikicin Boko Haram ya shafa.  Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya zai kawo ƙarshen ziyarar tasa tare da ganawa da manema labarai a gidan gwamnatin Maiduguri tare da gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum.  ...

Kaduna: Gumi Ya Kafa Ƙungiyar Kare Hakkin Makiyaya

Image
Kaduna: Gumi Ya Kafa Kungiyar Kare Hakkin Makiyaya Daga Ibrahim Ammani, Kaduna Rahoton daga jihar Kaduna na bayyana cewar mashahurin malamin addinin Musulunci Dakta Ahmad Gumi, ya sanar da cewa ya kafa ƙungiyar assasa kare hakkin Fulani makiyaya a Najeriya. Gumi ya bada sanarwar kafa ƙungiyar wacce za a ƙira ta da Nomadic Rights Concern (NORIC) a yayin rufe tafsirin watan Ramadan a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna. Ya ce ƙungiyar za ta tattaro tare da bayyana irin cin zarafi da take hakkokin Fulani makiyaya da ake yi, a kusan kullum a Najeriya. “Mun ga dacewar kafa Ƙungiyar ƙula da Hakkokin Makiyaya, NORIC, wacce za ta samu shugabancin Farfesa Umar Labbo. NORIC za ta zama wata hanya da makiyaya za su mika ƙorafinsu da damuwarsu zuwa ga hukumomin da suka dace. “Da yawa daga cikinsu sun yi ƙorafin cewa sun yi rashin ƴan uwansu. Wasu kuwa suna gidajen gyaran hali na tsawon shekaru ba tare da sun san laifukansu ba ko kuma na gurfanar da su. “An kafa wannan ƙungiyar ne domin magance wad...

Raunin Buhari Ne Ya Ƙara Girman Matsalar Tsaro – Shehu Sani

Image
Raunin Buhari Ne Ya Ƙara Girman Matsalar Tsaro – Shehu Sani Daga Ibrahim Ammani, Kaduna Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya ce saboda rashin jajircewar shugaban ƙasa ko kuma kunyarsa ta yi yawa akan na ƙasa da shi ne ya sa ya ƙasa kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro dake addabar ƙasar. Sani ya yi wannan maganar ne a ranar Asabar yayin da Daily Trust ta Twitter ta gayyace shi a matsayin bako mai jawabi inda ya yi magana akan rashin tsaro da kuma zaɓen 2023. “Mutanen da ke kan madafun iko su na ta gazawa kuma za su ci gaba da gazawa saboda shugaban ƙasar mu ba shida ƙarfin ɗaukar mataki akan na ƙasa da shi. “Idan ka jagoranci jami’an tsaro, sojoji, ko kuma ƙaramar hukuma ko jiha, kuma ana ci gaba da kai hare-hare yankinka, to ba ka da amfani kuma aikin shugaban ƙasa ne ƙorar irin wannan, ya maye gurbinsa da wani daban. “Wani lokaci matsalolin tsaro su na bukatar irin haka. Akwai zargin cewa har da jami’an tsaro ake hada kai ana rura wutar rashin tsaro wanda wannan babban lamar...