Skip to main content

Kaduna: Gumi Ya Kafa Ƙungiyar Kare Hakkin Makiyaya

Kaduna: Gumi Ya Kafa Kungiyar Kare Hakkin Makiyaya

Daga Ibrahim Ammani, Kaduna


Rahoton daga jihar Kaduna na bayyana cewar mashahurin malamin addinin Musulunci Dakta Ahmad Gumi, ya sanar da cewa ya kafa ƙungiyar assasa kare hakkin Fulani makiyaya a Najeriya.

Gumi ya bada sanarwar kafa ƙungiyar wacce za a ƙira ta da Nomadic Rights Concern (NORIC) a yayin rufe tafsirin watan Ramadan a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna.

Ya ce ƙungiyar za ta tattaro tare da bayyana irin cin zarafi da take hakkokin Fulani makiyaya da ake yi, a kusan kullum a Najeriya.

“Mun ga dacewar kafa Ƙungiyar ƙula da Hakkokin Makiyaya, NORIC, wacce za ta samu shugabancin Farfesa Umar Labbo. NORIC za ta zama wata hanya da makiyaya za su mika ƙorafinsu da damuwarsu zuwa ga hukumomin da suka dace.

“Da yawa daga cikinsu sun yi ƙorafin cewa sun yi rashin ƴan uwansu. Wasu kuwa suna gidajen gyaran hali na tsawon shekaru ba tare da sun san laifukansu ba ko kuma na gurfanar da su. “An kafa wannan ƙungiyar ne domin magance wadannan matsalolin kuma ana fatan makiyayan za su bi hanyar da ta dace wurin miƙa kokensu ba tare da tada hankula ba,”

Ya ce makiyayan za su iya miƙa korafe-korafensu ga NORIC, wanda zasu taimaka wurin daukan matakin shari’a don kwato musu hakkinsu.

Hakazalika Dr Gumi ya yi amfani da wa’azin wurin kira ga ‘yan bindiga da ke barna a ƙasar nan mussamman yankin arewa maso yamma da su rungumi zaman lafiya tare da ajiye makamansu. “Mun yi ƙira gareku da ku ji tsoron Allah tare da rungumar zaman lafiya. Kuyi koyi da wasu daga cikinku da suka ajiye makamai, suka saki waɗanɗa suka sace, suka tuba kuma suka nemi yafiyar Allah,”.

A kan farmakin jirgin ƙasa na Kaduna, malamin ya yi ƙira ga ƴan bindigan da su sako waɗanɗa suka sace tare da miƙa ƙorafinsu kai tsaye ga hukumomin da suka dace.

Comments

Popular posts from this blog

In Maiduguri, a 15-year-old girl was killed by a stray bullet from CJTF

The hospital has discharged minors who were victims of viral child abuse videos and they are currently recovering well.

BORNO: In Benishiekh, a man was killed during a tragic dispute over mango farming