Badaƙala: Ministar Kudi, ta kori Akanta-Janar na Najeriya.
Badaƙala: Ministar Kudi, ta kori Akanta-Janar na Najeriya.
Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta kori Akanta-Janar na Najeriya, Ahmed Idris daga mukaminsa saboda zargin badakalar Naira biliyan 80.
Matakin na zuwa ne kwana biyu bayan Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta cafke shi saboda zargin karkatar da kudaden.
Wasikar ta ce, Biyo bayan korarka da EFCC ta yi, saboda zargin karkatar da kudaden da yawansu ya kai Naira biliyan 80, ina sanar da kai cewa an dakatar da kai daga mukaminka daga ranar 18 ga watan Mayun 2022, ba tare da biyanka kowanne kudi ba.
“An dauki matakin ne don a samu damar aiwatar da cikakken bincike a kanka ba tare da katsa-landan ba, kamar yadda Dokokin Aikin Gwamnati suka tanadar.
"A iya tsawon wannan lokacin, ana so ka kauracewa ofishinka kuma kada ka halarci kowane irin taro ko ofishin gwamnati, har sai an gayyace ka,” inji wasikar.
Comments
Post a Comment