Raunin Buhari Ne Ya Ƙara Girman Matsalar Tsaro – Shehu Sani
Raunin Buhari Ne Ya Ƙara Girman Matsalar Tsaro – Shehu Sani

Daga Ibrahim Ammani, Kaduna
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya ce saboda rashin jajircewar shugaban ƙasa ko kuma kunyarsa ta yi yawa akan na ƙasa da shi ne ya sa ya ƙasa kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro dake addabar ƙasar.
Sani ya yi wannan maganar ne a ranar Asabar yayin da Daily Trust ta Twitter ta gayyace shi a matsayin bako mai jawabi inda ya yi magana akan rashin tsaro da kuma zaɓen 2023.
“Mutanen da ke kan madafun iko su na ta gazawa kuma za su ci gaba da gazawa saboda shugaban ƙasar mu ba shida ƙarfin ɗaukar mataki akan na ƙasa da shi.
“Idan ka jagoranci jami’an tsaro, sojoji, ko kuma ƙaramar hukuma ko jiha, kuma ana ci gaba da kai hare-hare yankinka, to ba ka da amfani kuma aikin shugaban ƙasa ne ƙorar irin wannan, ya maye gurbinsa da wani daban.
“Wani lokaci matsalolin tsaro su na bukatar irin haka. Akwai zargin cewa har da jami’an tsaro ake hada kai ana rura wutar rashin tsaro wanda wannan babban lamari ne da bai kamata a ƙyale shi ba.”
Ya ci gaba da cewa bai dace mutum ya zura ido yana ganin wanda ya dauka aiki yana zaune ba ya taɓuka abin kirki ba. Ya koka akan yadda gwamnati ta ƙara wa Shugaban Hukumar Gidajen Gyaran Halin Najeriya, shugabannin tsaro da sauransu wa’adi.
A cewarsa babu wata nasarar da aka samu bayan aiwatar da hakan kuma ya kamata shugaban ƙasa ya ƙara dagewa wurin yin aikinsa.
Comments
Post a Comment