Badaƙala; EFCC ta kama tsohon shugaban hukumar yankin Neja-Delta

Badaƙala; EFCC ta kama tsohon shugaban hukumar yankin Neja-Delta
 Daga A A Ngulde, Maiduguri
 
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC ya tsare tsohon shugaban hukumar yankin Neja-Delta Mista Nsima Ekere bisa zargin zamba da ƙuɗi naira biliya 47.

Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) a ranar Larabar da ta gabata sun kama tsohon Manajan Darakta na Hukumar Raya Yankin Neja-Delta (NDDC) Nsima Ekere bisa zargin karkatar da kudade da suka kai Naira biliyan 47 ta hannun ƴan kwangilar hukumar da suka yi rajista. 

Mai magana da yawun hukumar na NDDS Wilson Uwajaren ya tabbatar da hakan ne ga gidan talabijin na Channels. 

Shi dai tsohon shugaban hukumar ta NDDC ya kasance dan takarar gwamnan jihar Akwa Ibom na jam’iyyar All Progressives Congress  (APC) a zaben 2019. Ya kuma sha kaye a zaɓen fidda gwani na gwamna a jam’iyyar PDP a hannun Gwamna Emmanuel Udom a shekarar 2015. 

Nsima mai shekaru 56 d haihuwa ya kasance Manajin Darakta na hukumar tsakanin shekarar 2016 zuwa 2018.

 

Comments

Popular posts from this blog

In Maiduguri, a 15-year-old girl was killed by a stray bullet from CJTF

The hospital has discharged minors who were victims of viral child abuse videos and they are currently recovering well.

BORNO: In Benishiekh, a man was killed during a tragic dispute over mango farming