Ɗan Bindiga Ya Fi Deligate Imani – Shehu Sani
Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya ce babu maraban ƴan bindiga da ‘Deliget’ a siyasan Najeriya.
Shehu Sani ya bayyana cewa yadda mahara ke karɓar kuɗi a hannun waɗanda suka yi garkuwa haka suma ‘Deliget’ ke ƙarɓar irin wannan kuɗade a hannun mutane da sunan wai za su zaɓe su.
"Na shiga siyasa ne domin a gyara tsarin tare da tsaftace shi ta yadda za a rika zaɓen nagartattun mutane waɗanda suka cancanta ta hanyar yin zaɓen mai aminci da nagarta tun daga zaɓen ƴan takara zuwa zaɓen shugabanni.
"Ni fa a ganina ban faɗi zaben fidda gwani ba, ban yi nasara ne a kasuwanci siye da siyarwar ɗan takara ba ta hanyar wanda yafi zabga kuɗi ya kwashi dami.
"Bai kamata ace wai ta irin wannan hanya ce za a riƙa zaɓen waɗanda za su shugabanci jama’a a ƙasar nan ba, saboda maimakon a zaɓi nagari mai dammai a aljihu ne za a baiwa mulki ko mai lalacewar sa kuwa. Hakan bai dace ba.
"Gaba ɗaya turbar siyasar ƙasar nan a gurɓace ta ke, hanyar zaɓen ɗan takara ta hanyar zabe na ‘Deliget’ hanya ce kawai da ya bada damar ɗora ruɓaɓɓu, gurbatattun ƴan siyasa karagar mulki cikin sauki ta hanyar wadaƙar miliyoyin kuɗi.
"Idan ba mun dawo daga rakiyar siyasar mai-kudi-ɗauka bane komai munin sa ba za mu taba ɓanɓaro ƙasar nan daga bangon ginin cuwa-cuwa, almundahana, karfakarfa ba, sannan kuma matasa sai dai su ji a salansa amma ba wai su iya shiga a fafata da su ba.
Comments
Post a Comment