Shugaban Ƙasar Nijar Ya Haramta Wa Ministoci Ƙarin Aure

Shugaba Bazoum ya ce duk ministan da ke slda ɓuƙatar ƙarin aure to ya sauƙa daga muƙaminsa, a wani mataki da shugaban ya ce zai taimaka wajen rage yawan haihuwa barkatai a ƙasar.

Ya ce ya shaida wa ministocina cewa ya haramta musu ƙarin aure, matuƙar suna cikin gwamnatinsa.

“Idan akwai ministan da ke son yin ƙarin aure ba za mu hana shi ba, amma kuma wajibi ne ya sauƙa dama muƙamin Gwamnatin Tarayya,” inji Bazoum.

Bazoum ya sanar da gargadin ne a wurin wani taron mata da aka gudanar a ranar 13 ga watan Mayu, domin bikin ranar Mata da ake ui shekara-shekara, inda mahalarta suka yi ta shewa suna yabawa da wannan matakin.

Sai dai furucin shugaban sun tada jiniyar wuya a sassan Jamhuriyar Nijar, domin kuwa wani ɓangare ya caccaki shi a kan matakin da ya ɗauka na hana ƙarin aure.

Da yake jawabi, shugaba Bazoum ya ce yawan al’ummar Jamhuriyar Nijar na ƙaruwa, ta yadda hakan ke barazana ga jin dadin al’ummar ƙasar, ɓunƙasar masana’antu da kuma rayuwar yau da kullum.

Sannan ya nuna damuwa kan yadda maza ke ɗora wa mata nauyi, tare da ɓuƙatar ɗauƙar mataki kan irin halin tsanani da su shiga a cikin al’umma.


Comments

Popular posts from this blog

In Maiduguri, a 15-year-old girl was killed by a stray bullet from CJTF

The hospital has discharged minors who were victims of viral child abuse videos and they are currently recovering well.

BORNO: In Benishiekh, a man was killed during a tragic dispute over mango farming