Najeriya Na Buƙatar Megawat Dubu 100 Don Magance Matsalar Lantarki – Minista
Najeriya Na Buƙatar Megawat Dubu 100 Don Magance Matsalar Lantarki – Minista
Daga Adamu Aliyu Ngulde, Maiduguri
Tsohon Ministan Wutar Lantarki, Farfesa Barth Nnaji, ya ce Najeriya na buƙatar megawat dubu 100 na wuta in har ta na buƙatar magance matsalar wutar lantarki a ƙasa nan.
Nnaji ya bayyana hakan ne ranar Juma'a yayin ganawa da manema labarai a Enugu game da makomar wutar lantarki.
Ya ce ƙasar nan na fama da matsaloli a ɓangaren samar wa, yaɗa wa da rarraba wutar lantarki a ƙasa nan.
Ya ƙara da cewa wannan shi ne ya sanya zai yi wuya a samu isashshiyar wutar lantarki ga ƴan kasa.
Comments
Post a Comment