Fashewar Tukunyar Gas: Hukumomin tsaro sun tabbatar da mutuwar mutum huɗu A Kano

 Fashewar Tukunyar Gas: Hukumomin tsaro sun tabbatar da mutuwar mutum huɗu A Kano

     Kwamishinan Ƴan Sandan Jihar           Kano, Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya       ce an gano gawarwakin mutum            huɗu sannan yace jami’an tsaro          na ƙoƙarin gano ko akwai sauran        jama'a a cikin ɓaraguzan ginin            da iftila’in na safiyar Talata ya              rutsa da su.

Kwamishinan ya ce ba "bom ba ne, tukunyar gas ce ta fashe; akwai wani mai sana’ar walda da gas a nan, shi ne wanda abin ya fara kashewa.

“Zuwa yanzu an gano gawar mace ɗaya da maza uku kuma duk hukumomin tsaron da ke jihar Kano sun zo nan,” kama daga sojojin ƙasa, sojojin sama, DSS, da sauransau.

Kwamishinan Ƴan Sandan ya ce “za mu faɗaɗa bincike domin gano haƙiƙanin abin da ya faru.”


A wannan lamari dai ya faru ne a Titin Aba daura da Titin Kotu da ke Sabon Gari, wanda kawo yanzu ake ci gaba da gudanar aikin ceto.

An fitar da gawarwaki

Tun da farko, ganau sun shaida wa Aminiya cewa an fitar da gwara aƙalla mutum uku, ciki har da wani mai sana’ar walda a gaban makarantar firamare ta Winners daga cikin waɗanɗa abin ya rutsa da su.

Wani mazaunin unguwar ya yi iƙirarin cewa ya ga lokacin da abin yi tashi da wani mutum da ke tafiya akan layin abin da wasu ke zargin ɗan ƙunar ɓakin wake ne.

Shaidu sun tabbatar wa Jaridar Aminiya cewa ginin da ke wurin da abin ya yi bindiga ya ya tarwatse baki daya.


Hakazalika Jaridar Magarya ta gano cewa Bam ce ta fashe kamar yadda wasu shedun suka shaida mata.

Tuni jami’an tsaro da Jami’an Hukumar Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da takwarorinsu na Jihar Kano suka ziyarci wurin domin gudanar da aikin ceto.

Bidiyon wurin da abin ya faru ya nuna dandazon mutane na taimakawa wajen aikin ceto daga ɓaraguzan wani gini da abin ya shafa.

Idan za a iya tunawa dai a bara an samu makamanciyar wannan musiba inda wata tukunyar gas ta fashe a Unguwar Hotoro da ke Jihar Kanon, wadda ta yi sanadiyar jikkatar mutane da dama.


Comments

Popular posts from this blog

In Maiduguri, a 15-year-old girl was killed by a stray bullet from CJTF

The hospital has discharged minors who were victims of viral child abuse videos and they are currently recovering well.

BORNO: In Benishiekh, a man was killed during a tragic dispute over mango farming