Borno: Boko Haram Sun Kai Hari A Ƙauyen Kautikari
Borno: Boko Haram Sun Kai Hari A Kautikari
Daga Adamu Aliyu Ngulde, Maiduguri
Rahotanni daga ƙauyen Kautikari na ƙaramar hukumar Chibok dake kudancin jihar Borno na cewa wasu da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne sun kai haei da maraicin nan.
Da yake jawabi ga wakilinmu na jihar Borno DPO na Ƴan sandan ƙaramar hukumar Chibok ya tabbatar da faruwar lamarin. Inda yace "Dazu da yamma na samu labarin wasu mahara sun kai hari garin Kautikari kuma tuni jami'an ƴan sanda suka kai ɗaukin gaggawa sai dai har zuwa yanzun bamu san halin da ake ciki ba" Muna sa ran da safe zamu samu damar yin ƙarin kan abin da ya faru" inji shi.
Comments
Post a Comment