Shehun Borno ya nada sabon Shettima Mallumbe

Shehun Borno ya nada sabon Shettima Mallumbe
Mukhtar Alkali, sabon Shettiman Ilimi na ƙarbar takardar nadin sa 

Daga A A Ngulde, Maiduguri

Mai martaba Shehun Borno Alhaji Dr. Abubakar Ibn Umar Garbai Al-amin El-kanemi ya amince da naɗin Malam Mukhtar Alkali a matsayin Shettima Mallumbe na Borno, daya daga cikin manyan masu riƙe da sarautar gargajiya a masarautar daular Kanem Borno. 

Alhaji Grema Isa, (Grema Balbalbe) na Borno shi ne ya miƙa takardan naɗin a yayin hutun ƙarshen mako ga sabon mai riƙe da muƙamin.
Da yake gabatar da takardar nadin ga Mukhtar Alkali, Alhaji Grema ya ce naɗin Mukhtar Alkali ya kasance bisa cancanta domin ya gaji mahaifinsa marigayi Shettima Alkali Habib wadda ya rasu a shekarar da ta gabata.

Dimbin al'umma waɗanɗa zuri'ar Shettima Habib duk sun hallara tare da shaida miƙa takardan ga Mukhtar Alƙali. 
Da yake jawabi a madadin iyalan gidan marigayi Shettima Habib, Alhaji Bakura Mallam Lawan ya bayyana farin cikinsa sakamakon wannan naɗi na ɗan uwansa, inda yake cike da yabo ga Mai Martaba Shehun Borno, bisa ƙwarin gwiwar da aka yi wa iyalan marigayi Shettima Habib ta hanyar naɗa ɗansa Malam Mukhtar Alkali domin maye gurbin mahaifinsa da ya rasu. 
Alhaji Bakura ya kuma bada tabbatacin cewa Mukhtar Alƙali zai bakwa maraɗa kunya tare da tabbatar da amincewar da aka yi masa saboda yana da masaniyar ayyuka da sauran ayyuka na Shettima na Borno, yana mai jaddada cewa Mukhtar zai yi aiki tukuru da himma wajen tabbatar da amana da ƙwarin gwiwa da aka yi massa. 

Comments

Popular posts from this blog

In Maiduguri, a 15-year-old girl was killed by a stray bullet from CJTF

The hospital has discharged minors who were victims of viral child abuse videos and they are currently recovering well.

BORNO: In Benishiekh, a man was killed during a tragic dispute over mango farming