Tsaro: An Yi Wa Arewa Zobe– Zakzaky
Tsaro: An Yi Wa Arewa Zobe– Zakzaky
Daga Ibrahim Ammani, Kaduna
A sakon da ya fitar na murnar bikin sallah karama, Shugaban Ƙungiyar IMN (Shi’a) ta ƙasa Sheikh Ibrahim Yakubu El Zakzaky ya bayyana yadda maƙiya suka taso yankin Arewa
Shugaban ƙungiyar ta ‘yan Shi’a ya bayyana wasu abubuwa guda uku waɗanda sune jigajigan ƙarfin arzikin Arewa kuma ake burin ruguza su.
1-Noma. wadda ita ce tushen arzikin mutanen yankin, yanzu ta gagara, an hana manoma aiki an ƙore su daga garuruwan su, wanda ya zauna za a kashe shi.
2-Kiwo. Makiyaya an kashe ana kwashe dabbobin su.
3-Kasuwanci. Sufurin kayayyaki ya zama haɗari, saboda ayyukan ƴan ta’adda a hanyoyi. Sai gobara a kasuwanni wadda ba ta lafiya bace a rasa mai ya haddasa ta. Ɗan kasuwa idan yabi hanya a sace shi a nemi kudin fansa, sai dai a kwashe jarin sa a fanso shi ya dawo ba abin juyawa.
Su kuma manyan yankin ba wannan ne ya dame su ba, in dai za a ba mutum mukami shi kenan kawai.
Comments
Post a Comment