Skip to main content

Ƴan Bindiga Sun Sace Matafiya A Hanyar Abuja


Ƴan Bindiga Sun Sace Matafiya A Hanyar Abuja

          Daga Jaridar Magarya


Rahotannin daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa ƴan bindiga masu garkuwa da mutane sun sace matafiya da dama a hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Talata wani wanda ya shaida lamarin ya bayyana wa BBC cewa lamarin ya faru ne a garin Katari da misalin 4:30 na yammaci.

Ya bayyana cewa akwai motoci da dama waɗanda suna ajiye a ɓangaren zuwa Kaduna da aka yi awon gaba da masu motocin.

Ya kuma ce bayan faruwar lamarin jami’an tsaro masu ɗimbin yawa sun isa wurin domin kai ɗauki.

Muryar Ƴanci ta ruwaito cewa dukkanin kokarin da aka yi na jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ya ci tura saboda baya ɗaukar waya.

Comments

Popular posts from this blog

In Maiduguri, a 15-year-old girl was killed by a stray bullet from CJTF

The hospital has discharged minors who were victims of viral child abuse videos and they are currently recovering well.

BORNO: In Benishiekh, a man was killed during a tragic dispute over mango farming