Sakatare Janar na MDD ya ziyarci Maiduguri
Sakatare Janar na MDD ya ziyarci Maiduguri
Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ziyarci birnin Maiduguri sannan ya gana da Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum da kuma nabban jami’in Majalisar Dinkin Duniya kana mai kula da ayyukan jin ƙai Mista Mathias Schmale a filin jirgin saman Maiduguri.
Hakazalika sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ziyarci Maiduguri babban birnin jihar Borno da yammacin yau a ci gaba da ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Najeriya.
Wakilinmu Adamu Ngulde ya ruwaito mana cewa ana sa ran Mista Guterres zai tattauna da mai masaukin baƙi Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum da kuma tattauna da tuɓaɓɓun mayaƙan da suka miƙa wuya da waɗanɗa rikicin Boko Haram ya shafa.
Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya zai kawo ƙarshen ziyarar tasa tare da ganawa da manema labarai a gidan gwamnatin Maiduguri tare da gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum.
Wakilinmu Adamu Aliyu Ngulde ya ruwaito mana cewa, tun da farko dai Mista Guterres ya kai ziyara Jamhuriyar Nijar da kuma ƙasar Senegal sannan a yau Talata ya kai ziyarar a birnin Maiduguri.
Comments
Post a Comment