Skip to main content

Hukumar EFCC Ta Damke Akanta Sakamakon Harƙarlan Biliyan 80.


Hukumar EFCC Ta Damke Akanta Sakamakon Harƙarlan Biliyan 80.

Rahotannin daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta kama Akanta Janar na tarayya bisa zarginsa da almundahana ta naira biliyan 80.

Hukumar ce ta bayyana haka a shafinta na Facebook inda ta ce ta kama shi a ranar Litinin 16 ga watan Mayun 2022.

Hukumar na zargin Ahmed Idris da karkatar da kuɗin ta hanyar amfani da abokansa da iyalai da sauran hanyoyi.

EFCC ta ce an yi amfani da kuɗin wurin gina rukunin gidaje a Kano da Abuja.

Ta kama Idris ne bayan ya ƙi ƙarɓar gayyatar da EFCC ta rinƙa aika masa domin tuhumarsa kan zarge-zargen da ake yi masa, kamar yadda hukumar ta bayyana.

Comments

Popular posts from this blog

In Maiduguri, a 15-year-old girl was killed by a stray bullet from CJTF

The hospital has discharged minors who were victims of viral child abuse videos and they are currently recovering well.

BORNO: In Benishiekh, a man was killed during a tragic dispute over mango farming