Karon Farko Cikin Shekara 11 AC Milan Ta Lashe Gasar Serie A
Nasarar Milan na zuwa ne bayan ta doke Sassuolo da ci 3-0 a wasan ranar ƙarshe na gasar Serie A da aka fafata a Yammacin ranar Lahadi.
Milan dai ta lashe hasar ne ita kuma babbar abokiyar hamayyarta, Inter Milan ta kare a mataki na biyu da tazarar maki biyu tsakaninsu.
Ƴan wasan na Stafano Pioli sun jinjina kofin duk da nasarar da Inter ta yi 3-0 kan Sampdoria.
Olivier Giroud ne ya zira ƙwallo biyu a wasan kafin daga baya Frank Kessie ya zura ta uku duk a cikin minti 36 da fara wasan.
Karo na 19 ke nan jimilla da Milan wadda ake yi wa laƙabi da Rossoneri ta lashe babbar gasar Italiya ta Serie A a tarihi.
Comments
Post a Comment