Sojoji Sun Ragargaza Sansanonin ISWAP A Borno
Sojojin runduna ta 198, sun gudanar da gagarumin aikin ne tare da hadin gwiwar dakarun haɗin gwiwa na ƙasa da ƙasa (MNJTF) dake yankin tankin Chadi, domin fatattakar ƴan ta’addan a ƙaramar Hukumar Kukawa dake arewacin Jihar Borno.
Wani jami’in leƙen asiri, ya ce yankunan da sojojin suka kwace a hannun mayaƙan ISWAP su ne Kangarwa, Alagarno, Daban Masara, Kwatan Daban Masara, Grede, Makar, Daban Karfe, Bulawa, Daban Gajere, Kwatan Garba, Ali Sharafti da kuma Tamfalla (kasuwar kifi) daga hannun ƴan ta’addan.
Majiyar ta shaida wa Zagazola Makama, ƙwararre kan yaki da tada kayar baya, kuma manazarcin harkokin tsaro a yan Tafkin Chadi, cewa an ƙashe wasu ƴan ta’addar da ba a tantance adadinsu ba a lokacin da sojojin suka kai farmaki maɓoyarsu kuma da yawa daga cikinsu suka gudu suka bar kayansu.
Majiyar Jaridar Magarya sun bayyana cewa a ci gaba da kai hare-hare ta ƙasa da jiragen yaki a yankin, inda dakarun Rundunar Desert Sanity da MNJTF Lake Sanity suka yi ya yi matukar matsin lamba kan mayaƙan tare da kawo musu na ƙasu.
A cewarsa, sojojin tare da haɗin gwiwar dakarun ƙawancen ƙasashen Chadi, Nijar da kuma Kamaru suka yi ta kai hare-hare babu ƙaƙƙautawa ta hanyar leƙen asiri, wanda ya yi sanadin mutuwar ƴan ta’addar masu yawan gaske, ciki har da manyan kwamandojinsu da kuma yadda aka tarwatsa matsugunansu baki daya.
“Galibin mayaƙan da iyalansu sun yi watsi da makamansu sakamakon matsanancin matsin lamba da rashin magani ga waɗanɗa suka samu raunuka;
“’Ƴan ta’addan da suka tsira kuma an tilasta musu tserewa zuwa sansanonin wucin gadi da aka kafa a wuraren da suka mayar mafakarsu.
“Majiyar ta ƙara da cewa tuni ƴan ta’addan sun garzaya zuwa magudanar ruwa na Daban Masara kuma a halin yanzu suna ɓuya a yankunan Sabon Tumbu, Tudun Wulgo, Kusuma da Sigir na Marte da Ngala.
An gano wasu mayaƙan a cikin kwale-kwale tare da iyalansu yayin da suke ƙoƙarin tserewa ta hanyar Kaduna Ruwa da Kandahar da ke iyakar jamhuriyar Nijar da Chadi,” in ji majiyar.
Comments
Post a Comment