Rundunar Ƴan sandan Jihar Borno Ta Tarwatsa Nakiya A Sansanin Dalori

Rundunar Ƴan sandan Jihar Borno Ta Tarwatsa Nakiya A Sansanin Daori
Daga Adamu Aliyu Ngulde, Maiduguri

Rundunar ƴan sandan jihar Borno tayi nasarar tarwatsa nakiya da wasu maƙiya zaman lafiya suka ɗana a sansanin ƴan gudun hijira na Dalori dake hanyar Maiduguri zuwa ƙaramar hukumar Bama.

Wannan sansani na Dalori mai nisan kilomita goma daga birnin Maiduguri ya ƙunshi ƴan gudun hijira masu yawan gaske da samun mafaka tsawun shekaru sakamakon hare-haren mayaƙan Boko haram da ya raba su da muhallinsu.
Ƙwamishinan ƴan sandan jihar Borno Abdu Umar ne ya bayyana hakan yayin da yake yiwa manema labarai ƙarin bayani kan nasarar da ayarin ƴan sanda masu kunce bama-bamai suka yi da safiyar ranar Litinin.

Yace domin daƙile barazanar da wasu ɓata gari ke yi domin tada husuma a tsakanin al'umma, ƙwararrun sun garzaya wurin da sanyin safiyar ranar Litinin tare da yin bincike a yankin sun kuma samu sa'ar tarwatsa wa da kuma kwashe raguwar bama-baman da aka dasa domin kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba. 
Hakazalika Kwamishinan ya kuma bayyana farin ciki sakakamon ƙoƙarin da jami'ansu suka yi da zummar kare rayukan al'ummar wannan sansanin.

 Har ila yau Abdu Umar ya umurci al'ummar wannan sansani na Dalori  da su ci gaba da lura da muhallinsu saboda ƴan ta'addan za su yi amfani da wannan damar domin haddasa haifar da tashin-tashina.

Comments

Popular posts from this blog

In Maiduguri, a 15-year-old girl was killed by a stray bullet from CJTF

The hospital has discharged minors who were victims of viral child abuse videos and they are currently recovering well.

BORNO: In Benishiekh, a man was killed during a tragic dispute over mango farming