Taraba: Sabon Rikici Ya Kunno Kai A Jam’iyyar APC

Taraba: Sabon Rikici Ya Kunno Kai A Jam’iyyar APC

          BASHIR ADAMU, JALINGO

Wani sabon rikici ya ɓarke a Jam’iyyar APC ta Jihar Taraba sakamakon sauya zaɓaɓɓun Shugabannin Ƙananan Hukumomi guda hufu.

A ranar Asabar ne Jam’iyyar APC ta sake rantsar da wasu sabbin Shuwagabannin ƙananan hukumomin Ussa, Wukari, Ibi da Takum.

Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Taraba, Ibrahim Tukur El-sudi ne ya jagoranci rantsarwan, inda wasu bayanai ke cewa yayi hakan ne bisa umurnin Uwar Jam’iyyar ta ƙasa da ta turo mishi da sunayen waɗannan sabbin Shugabanni guda huɗu.

Inda yace waɗannan zaɓaɓɓun Shugabannin da aka sauya, su daina bayyana kansu a matsayin shugabannin Jam’iyyar domin tuni aka yi waje rot dasu, duk da cewa ba’a bayyana laifin da suka yi aka ciresu ba.

Sai dai kuma a wani mataki na maida martani game da matakin na El-sudi, ƙungiyar ƴakin neman zaɓen Gwamnan Jihar Taraba na David Sabo Kente, sun shaidawa Shalkwatan Jam’iyyar APC na ƙasa da su gaggauta wannan yunƙurin canjin shugabannin da sukayi batare da wani laifi ba, ko kuma su ƙalubalanci matakin a Kotu, kamar yanda shugaban ƙungiyar, Abba Akawu- Zaga ya aiyana yayin ganawanshi da manema labarai a ranar Lahadi.

"An kori Shugabannin Jam’iyya na ƙananan Hukumomi huɗu, babu gaira babu dalili waɗan da aka zaɓesu tare da shuwagabannin zartarwar Jiha, toh ku sani waɗanda aka rantsar a ‘jiya’ ba zaɓaɓɓu bane, kuma bamu san suba, kuma Kundin tsarin malkin Jam’iyya bai san da suba a hukumance, hakan yin karan tsaye ne ga Jam’iyyan da ba zai haifar da ɗa mai ido ba.

Akawu- Zaga ya ankarar da Jam’iyyar cewa dole su tuna da haɗarur-rukan dake tattare da rashin samun nasaran Jam’iyyar a zaɓen da ya gabata na Shekara ta 2019 da kuma na 2023 dake tafe.

Comments

Popular posts from this blog

In Maiduguri, a 15-year-old girl was killed by a stray bullet from CJTF

The hospital has discharged minors who were victims of viral child abuse videos and they are currently recovering well.

BORNO: In Benishiekh, a man was killed during a tragic dispute over mango farming