Manchester City Ta Lashe Gasar Firimiyar Ingila
Wannan shi ne dai karo na shida da ƙungiyar ta lashe gasar a tarihi.
Ƙungiyar da Pep Guardiola ke jagoranta ta kare kakar ta bana da tazarar maki daya kacal tsakaninta da Liverpool, wadda ta doke Wolves 3-1 a wasan ƙarshen da aka fafata a Yammacin ranar Lahadi.
Ƙwallo biyu da Ikay Gundogan ya ci da kuma wadda Rodri ya zira a cikin minti shida kacal su ne suka bai wa City nasara inda ta lashe wasan da 3-2.
Villa ta shiga gaba a wasan tun farko ta hannun Matty Cash da Philippe Coutinho.
Comments
Post a Comment