Yau ce Ranar Yaƙi Da Cutar Yoyon Fitsari
Yau ce Ranar Yaƙi Da Cutar Yoyon Fitsari
Daga Jaridar Magarya
Ranar 23 ga watan Mayun kowace shekara wasu Kungiyoyin da ke aikin jin ƙai sun ɗauki matakin magance matsalar tsakanin mata musamman waɗanɗa ke fama da matsalolin tsaro.
Yayinda ake gudanar da bikin ranar yaki da cutar yoyon Fftsari da nufin kawo ƙarshen ta a cikin al’umma wasu ƙungiyoyin da ke aikin jin ƙai sun ɗauki matakin magance matsalar a tsakanin mata.
Taken bikin na bana shi ne ƴancin Mata ‘Ƴan bani Adama ne a kawo ƙarshen cutar Yoyon Fitsari.”
Matsalar Yoyin fitsari ta na zama ruwan dare gama duniya a Najeriya inda ake samun ƙaruwar matsalar cutar ta yoyon fitsari inda ta shafi rayuwar dubun dubatar Mata.
Baki ya zo daya tsakanin Masana kiwon lafiya da masharhanta har da masu yaki da wannan matsalar inda su ke alaƙanta ƙaruwar ta da jahilci da kuma matsalolin da ake samu lokacin haihuwa da ma Auren wuri da ake yiwa wasu ƴan Mata da ba su tasa ba.
Dubun dubatar Mata sun shiga cikin mawuyacin hali sanadiyyar samun wannan matsala inda ake ƙyamar su ba kawai kawaye ko makobta ba har ƴan uwa da ma wasu mazajen auren su.
Akwai Mata da dama da auren su ya mutu saboda wannan lalura da ta same su wanda ba laifi ba ne kamar yadda masana su ka bayyana.
Malama Fatima Iya Abba Mustpha daya daga cikin waɗanɗa su ka sha fama da wannan Lalura ta yoyon Fitsari ce wacce kuma ta rasa auren ta har sau biyu.
To sai dai yanzu haka a na samun ƙungiyoyin da ke share hawayen irin waɗannan Mata ta hanyar taimaka masu a warkar da su daga wannan matsala kuma a koya mu su sana’o’in dogaro da kai.
Akwai ɗaruruwan Mata da su ka mori irin wannan tallafi kyauta wanda Kungiyar Coika da UNFPA suka samar a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.
Na daga cikin waɗanda su ke taimawa irin wannan mata, Mista Kelvin Chukwuemeka wani jami’in waɗan nan ƙungiyoyi ne da ke aikin bada tallafi na magance Lalurar Yoyon Fitsari ya yi ƙarin bayani kan ayyukan na su.
Ya ce "Wannan shirin bada tallafi ya taimakawa Mata ƴan mata da yawa. Daya daga cikin manyan ayyukan tallafin shi ne samar da cibiyar kula da masu yoyin Fitsari mai gadaje 40 a asibitin ƙwararru na Maiduguri. Kuwa ita wannan cibiya ba kawai ga Mutanen jihar Borno ba ce a'a, ta na taimakawa mata daga jihohin Yobe da Adamawa da ma wasu ƙasashe makobta.
Yanzu haka ana kan yiwa Mata aikin gyaran wannan Lalura a wannan cibiyar. "Haka kuma mu na bayar da horo ga ƙwararrun likitoci da ake aikin gyara. Bayan yi wa mata aikin gyara wannan lalura kuma ana horar da su sana’o’in dabam-dabam……”
A iya cewa dai kwalliya na biyan kudin sabulu inda a kullum ake magance irin waɗan nan Mata matsalolin su abun da ya sa masu rajin kare hakkin Mata ke yin ƙira da a kara faɗakar da al’umma wannan lalura da kuma yadda za su amfana da ayyukan waɗan nan ƙungiyi da ke taimakawa.
Comments
Post a Comment