Jonathan ya yi watsi da fom din takarar da aka saya masa
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya nesanta kan sa daga wadanda suka ce sun saya masa fom domin tsayawa takarar shugaban kasar zaben da za a yi a shekara mai zuwa a karkashin Jam’iyyar APC mai mulki.
Wata sanarwar da mai magana da yawun sa Okechukwu Eze ya rabawa manema labarai ta ce Jonathan bashi da wata masaniya game da saya masa takardar takarar kuma bashi da wata alaka da wadanda suka ce sun saya masa.
Sanarwar ta bukaci 'yan Najeriya da su yi watsi da rahotanni cewar zai tsaya takara a Jam’iyyar APC duk da ya ke sun san cewa wasu daga cikin kiraye kirayen da ake wa tsohon shugaban na da matukar tasiri.
Tun farko dai wata kungiyar ‘yan arewacin Najeriya da ake dangantawa da Fulani ce ta sanar da biyan Jam’iyyar APC naira miliyan 100 domin karbar fom din takarar zaben shugaban kasar da sunan Goodluck Jonathan, matakin da ya haifar da cece kuce a ciki da wajen Najeriya.
Ko a kwanakin baya sai da wasu matasa su ka yi zanga zangar lumana a Abuja babban birnin Najeriyar wadanda suka yi tattaki zuwa ofishin Jonathan tare da bukatar shi ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a zaben na 2023.
Comments
Post a Comment