Buhari Ya Yi Tir Da Kisan Deborah A Sokoto
Buhari Ya Yi Tir Da Kisan Deborah A Sokoto

Daga Ibrahim Ammani, Kaduna
Shugaban Ƙasa Buhari ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyayen ɗalibar kwalejin Shehu Shagari dake Sokoto wanda ajali ya iske ta bayan an zarge ta da yin kalaman ɓatanci ga Annabi SAW.
Buhari ya ce doka ba ta ba wani damar yanke hukunci kai tsaye ba. komai na da hurumin sa.
Idan an yi laifi sai kuma a bari waɗanɗa hukunci ke hannunsu su yanke shi ba kowa ya yi gaban kansa ba.
A sakon da ya fitar wanda kakakin shugaban Garba Shehu ya saka wa hannu, Buhari ya yabawa wa gaggawar ɗaukar mataki da gwamnatin Sokoto ta ta yi a lokacin da abin ya auku.
"Babu wanda yake da damar yanke hukunci ko ɗaukar doka a hannun sa a ƙasar nan. Tashin hankali ba zai haifar da ɗa nai ido ba.
Comments
Post a Comment