Sarkin Musulmi Ya Bada Umarnin Duba Watan Karamar Sallah Daga Ibrahim Ammani Fadar Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ta fitar da wata sanarwar da ke ƙira ga Musulman Najeriya su fara neman sabon watan Shawwal daga yau Asabar. Sanarwar wadda Arc. Zubairu Haruna Usman-Ugwu – wanda shi ne shugaban gudanarwa na hukumar NSCIA – ya sanya wa hannu, ta ce “Kwamitin Ganin Wata na ƙasa (NMSC), Sarkin Musulmi ya umarci al’ummah Musulmi a Najeriya su fara duba sabon watan Shawwal daga Asabar 30 ga watan Afrilu 2022, wanda yayi daidai da 29 ga watan Ramadan, 1443 AH. Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Idan Musulmai masu daraja suka ga jinjirin watan, sai Mai Alfarma Sarkin Musulmi zai sanar da ranar Lahadi 1 ga watan Mayun 2022 a matsayin ranar 1 ga watan Shawwal kuma ranar eid-fitr kenan. Amma, idan ba a ga jinjirin watan ba a wannan ranar, ranar Litinin 2 ga watan Mayun 2022 ta zama ranar Idul Fitr ke nan. A ƙarshe sanarwar ta ce ana iya tuntuɓar dukkan jagororin al’umma a dukkan sassa...