Eid-el-Fitr: Hukumar SEMA ta tallafawa ‘yan gudun hijira
Eid-el-Fitr: Hukumar SEMA ta tallafawa ‘yan gudun hijira
Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA) Hajiya Yabawa Kolo ta rabawa ƴan gudun hijira kayan abinci
Daga Adamu Aliyu Ngulde, Maiduguri
Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA) Hajiya Yabawa Kolo ta ƙaddamar da rabon kayan abinci ga ‘yan gudun hijira a sansanin Gubio da ke wajen birnin Maiduguri, gabanin bikin ƙaramar Sallah da ke tafe.
Da take jawabi yayin rabon kayan abinci a ranar Asabar, Yabawa Kolo ta ce kayan da hukumar ta rabawa ƴan hijirar gudumuwa ce da Gwamna Babagana Zulum ya bada umarnin a rabawa marasa galihu.
Ta kuma jaddada cewa sansanin ‘yan gudun hijira na Gubio yana daya daga cikin sansanonin ‘yan gudun hijira mafi girma a halin yanzu a cikin birnin Maiduguri da ke da ‘yan gudun hijira sama da dubu 10,000 biyo bayan rufe wasu sansanonin ‘yan gudun hijira da gwamnatin jihar Borno ta yi tare da sake tsugunar da ‘ya hijirar ta hanyar da ta dace.
Ta kara da cewa gwamnatin jihar tana kuma yin iyaka iyawarta domin ganin an rufe ƴan tsirarun sansanonin ‘yan gudun hijira nan da wani lokaci, inda ta bukaci ‘yan gudun hijirar da su ƙara ƙaimi wajen addu’o’i ga shugabannin jihar.
Shugaban Hukumar SEMA ta ƙara jaddada ƙudirinta na samar da ayyukan jin kai ga ‘yan gudun hijirar a dukkan sassan jihar tare da yin alƙawarin yin hulda da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta kasa NEMA, Hukumar Raya Arewa maso Gabas (NEDC) da sauran ƙungiyoyin agaji na tarayya.
Hakazalika ta yabawa Gwamnan Jihar Zulum bisa yadda yake tallafa wa hukumar domin ganin an rabawa ƴan hijirar.
Tun da farko da yake jawabi, Shugaban Kwamitin Rarraba kayan, Ali Abdullahi Isa ya ce an raba kayyakin inda aka yi amfani da umarnin Babban Daraktan da aka ajiye a babban ɗakin adana abinci na SEMA. Sai dai ya yi alƙawarin raba kayayyakin bisa ga adadin ‘yan gida da ke kowane sansanonin yayin da ya yaba wa Darakta Janar na SEMA bisa ƙoƙarinta na zaƙulo waɗanɗa suka cancanta domin su yi aiki a kwamitin.
Cikin jawabinsa shugaban sansanin ‘yan gudun hijira na Gubio, Mustapha Mohammed ya godewa gwamna Babagana Umara Zulum da kuma hukunar ta SEMA sakamakon yadda suke damuwa da halin da ‘yan gudun hijirar ke ciki, ya kara da cewa, a shirye suke su koma muhallinsu na asali da koda yaushe domin ci gaba da rayuwarsu ta yau da kullum.
Kayayyakin da aka raba sun hada da man girki, gishiri, maggi, buhunan gero, kuɓewa da tumaturi da dai sauransu.
Comments
Post a Comment