DSS Ta Bankaɗo Shirin Tayar Da Bama-Bamai Lokutan Bikin Sallah


Daga Ibrahim Ammani

Rahotannin daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar ‘Yan Sandan farin kaya ta DSS ta bayyana gano shirin kai hari akan wuraren ibada da wuraren shakatawa da kuma wasu kadarorin gwamnati musamman lokacin bikin Sallah da bayan sa.


Mai Magana da yawun Hukumar Peter Afunanya ya bayyana haka a sanarwar da ya rabawa manema labarai, inda yake zargin mutanen cewar suna shirin mayar da kasar irin halin da ta samu kanta kafin shekarar 2015 inda ake samun fashe fashen makamai.

Jami’in ya bukaci jama’a da su zuba ido domin lura da abubuwan da suke faruwa a yankunan su, yayin da suke gudanar da harkokin su na yau da kullum, tare da gabatarwa jami’an tsaro da bayanan duk wani abinda basu gamsu da shi ba a yankunan su.

Comments

Popular posts from this blog

In Maiduguri, a 15-year-old girl was killed by a stray bullet from CJTF

The hospital has discharged minors who were victims of viral child abuse videos and they are currently recovering well.

BORNO: In Benishiekh, a man was killed during a tragic dispute over mango farming