Da Ɗumi-Ɗumi: Sarkin Oyo mai mata barkatai, Oba Lamidi, ya rasu
Da Ɗumi-Ɗumi: Sarkin Oyo mai mata barkatai, Oba Lamidi, ya rasu
Rahotanni daga jihar Oyo na nuni da cewa Allah ya yiwa Sarkin Oyo rasuwa. Basarake mafi girma a ƙasar Yarbawa, Oba Lamidi Adeyemi ya rasu da yammacin ranar Juma'a a Asibitin koyarwa na jami'ar Afe Babalola dake Ado Ekiti.
Tsadar daren ranar Juma'a ne aka gaggauta kai gawarsa jihar Oyo domin fara shirin jana'izarsa.
Marigayi Adeyemi ya rasu yana da shekaru 83 bayan kwashe shekaru 52 kan mulki.
Comments
Post a Comment