Zaɓen 2023: ƙungiyoyi 150 sun ɓuƙaci Zulum tsayawa takara karo na biyu.
Zaɓen 2023: ƙungiyoyi 150 sun ɓuƙacu Zulum ya tsayawa takara karo na biyu.
Daga Adamu Aliyu Ngulde, Maiduguri
Zaɓen 2023: Ƙungiyoyi a birnin Maiduguri 150 sun tsaida aniyar tarawa Zulum miliyan 50 don takarar gwamna ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC.
Jaridar Magarya ya bayar da rahoton cewa, gamayyar ƙungiyoyin da suka fito da wannan matsayar sun bayyana aniyar su ne ranar Juma'a yayin taron manema labarai da suka gudanar a sakatariyar ƙungiyar ƴan jaridu da ke birnin Maiduguri.
Mai magana da yawun ƙungiyar Umar Shettima, ya ce ƙungiyoyin suna da muradin gwamna Babagana Umara Zulum ya ci gaba da zama a kan karagar mulki bisa la’akari da irin ayyukan da ya yi a wa’adinsa na farko.
Sannan yace ƙungiyoyin sun ƙunshi ƙwararrun malamai, ma'aikatan kiwon lafiya, sufuri da ƙungiyoyin mata da dai sauransu.
Hakazalika sun buƙaci al’ummar jihar Borno da su mara musu goyon bayansu ta hanyar bayar da gudumawar siyar fom domin ana buƙatar kudi yayin yaƙin neman zaɓe.
Kawo yanzu dai Jaridar Magarya ya bada rahoton cewa, har ya zuwa safiyar yau Asabar dai babu wani ɗan takara da ya nuna sha’awar tsayawa takarar Gwamna ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC.
Comments
Post a Comment