Fashewar bama-bamai ya sanya firgici a zuƙatan mazauna birnin Maiduguri.

Ƙarar fashewar wasu abubuwa da ake kyautata zaton cewa bama-bamai ne sun sanya firgici a zuƙatan mazauna birnin Maiduguri.

Daga Yasir Sabo, Maiduguri

Kafar jaridar YERWA EXPRESS ta ruwaito cewa majiyoyin tsaro masu sahihanci sun shaida mata cewa ƙarar fashewar daga ɓangaren jami'an tsaro soji ne suna tauna tsakua ne domin aya taji tsoro.

Wani jami’in Sa kai na ƙungiyar Civilian JTF ya shaidawa Yerwa Expresd cewa "a daren nan an ga shawagin ‘yan Boko Haram/ISWAP a kusa da garin Kayamla shi yasa jami'an tsaron suka yi shirin ko ta kwana.

Yace a halin yanzu 'yan ta'addan sun yi ƙone-ƙone a ƙauyen na Kayamla don haka sojoji suka yi shiri tsab "kuma wannan Fashe-fashen da kuke ji daga sojojinmu ne domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma" inji majiyar.

Comments

Popular posts from this blog

In Maiduguri, a 15-year-old girl was killed by a stray bullet from CJTF

The hospital has discharged minors who were victims of viral child abuse videos and they are currently recovering well.

BORNO: In Benishiekh, a man was killed during a tragic dispute over mango farming