Mutuwar Oyo Adeyemi Babban Rashi Ne Ga Najeriya- Buhari
Mutuwar Oyo Adeyemi Babban Rashi Ne Ga Najeriya- Buhari

Daga Ibrahim Ammani
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa gwamnatin Jihar Oyo da al’ummar jihar sakamakon rasuwar sarkin Yarabawa madi girma Alafin na Oyo, Lamidi Olayiwola Adeyemi III, ranar Juma’a.
A ranar Asabar aka yi jana’izar sarkin a tsohon garin Oyo, inda aka binne shi a farfajiyar masarautarsa.
Marigayin ya rasu yana da shekaru 83 a wani asibiti da ke jihar Ekiti bayan ya yi fama da jinya.
Comments
Post a Comment