Posts

Eid El-Fitr: Anga jinjirin watan Shawwal a Nijar

Image
Daga Adamu Aliyu Ngulde, Maiduguri Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa za a yi bikin ƙaramar Sallah a gobe Lahadi, bayan ganin jinjirin watan Shawwal a sassan ƙasar.

Eid-el-Fitr: Hukumar SEMA ta tallafawa ‘yan gudun hijira

Image
Eid-el-Fitr: Hukumar SEMA ta tallafawa ‘yan gudun hijira    Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA) Hajiya Yabawa Kolo ta rabawa ƴan gudun hijira kayan abinci Daga Adamu Aliyu Ngulde, Maiduguri Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA) Hajiya Yabawa Kolo ta ƙaddamar da rabon kayan abinci ga ‘yan gudun hijira a sansanin Gubio da ke wajen birnin Maiduguri, gabanin bikin ƙaramar Sallah da ke tafe. Da take jawabi yayin rabon kayan abinci a ranar Asabar, Yabawa Kolo ta ce kayan da hukumar ta rabawa ƴan hijirar gudumuwa ce da Gwamna Babagana Zulum ya bada umarnin a rabawa marasa galihu. Ta kuma jaddada cewa sansanin ‘yan gudun hijira na Gubio yana daya daga cikin sansanonin ‘yan gudun hijira mafi girma a halin yanzu a cikin birnin Maiduguri da ke da ‘yan gudun hijira sama da dubu 10,000 biyo bayan rufe wasu sansanonin ‘yan gudun hijira da gwamnatin jihar Borno ta yi tare da sake tsugunar da ‘ya hijirar ta hanyar da ta...

Sarkin Musulmi Ya Bada Umarnin Duba Watan Karamar Sallah

Image
Sarkin Musulmi Ya Bada Umarnin Duba Watan Karamar Sallah Daga Ibrahim Ammani Fadar Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ta fitar da wata sanarwar da ke ƙira ga Musulman Najeriya su fara neman sabon watan Shawwal daga yau Asabar. Sanarwar wadda Arc. Zubairu Haruna Usman-Ugwu – wanda shi ne shugaban gudanarwa na hukumar NSCIA – ya sanya wa hannu, ta ce “Kwamitin Ganin Wata na ƙasa (NMSC), Sarkin Musulmi ya umarci al’ummah Musulmi a Najeriya su fara duba sabon watan Shawwal daga Asabar 30 ga watan Afrilu 2022, wanda yayi daidai da 29 ga watan Ramadan, 1443 AH. Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Idan Musulmai masu daraja suka ga jinjirin watan, sai Mai Alfarma Sarkin Musulmi zai sanar da ranar Lahadi 1 ga watan Mayun 2022 a matsayin ranar 1 ga watan Shawwal kuma ranar eid-fitr kenan. Amma, idan ba a ga jinjirin watan ba a wannan ranar, ranar Litinin 2 ga watan Mayun 2022 ta zama ranar Idul Fitr ke nan. A ƙarshe sanarwar ta ce ana iya tuntuɓar dukkan jagororin al’umma a dukkan sassa...

Fashewar bama-bamai ya sanya firgici a zuƙatan mazauna birnin Maiduguri.

Image
Ƙarar fashewar wasu abubuwa da ake kyautata zaton cewa bama-bamai ne sun sanya firgici a zuƙatan mazauna birnin Maiduguri. Daga Yasir Sabo, Maiduguri Kafar jaridar YERWA EXPRESS ta ruwaito cewa majiyoyin tsaro masu sahihanci sun shaida mata cewa ƙarar fashewar daga ɓangaren jami'an tsaro soji ne suna tauna tsakua ne domin aya taji tsoro. Wani jami’in Sa kai na ƙungiyar Civilian JTF ya shaidawa Yerwa Expresd cewa "a daren nan an ga shawagin ‘yan Boko Haram/ISWAP a kusa da garin Kayamla shi yasa jami'an tsaron suka yi shirin ko ta kwana. Yace a halin yanzu 'yan ta'addan sun yi ƙone-ƙone a ƙauyen na Kayamla don haka sojoji suka yi shiri tsab "kuma wannan Fashe-fashen da kuke ji daga sojojinmu ne domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma" inji majiyar.

EID-EL-FITR: POLICE IN BORNO COMMIT TO PROTECT LIVES, PROPERTY

Image
EID-EL-FITR: POLICE IN BORNO COMMIT TO PROTECT LIVES, PROPERTY   By  Adamu Aliyu Ngulde, Maiduguri Borno State Police Command reitetates its commitment to protect lives and properties during and after Eid-El-Fitr Festivities. The state Police Public Relation Officer PPRO ASP Sani Kamilu Muhammad Shatambaya stated this in an interview in his office in Maiduguri. This comes after terrorists threatened to detonate bombs in Maiduguri, Bama and Konduga local government areas during sallah celebration. The Police Command reiterated its redness to provide adequate security for lives and property before, during and after the forthcoming Eid-El-Fitr celebration and assures  of sufficient deployment of Police personnel to EID praying grounds, and other public places across the state to ensure the safety of residents during the celebration and beyond. The Police Public Relations Officer said the Command will not hesitate to clamp down on any miscreant who may want to use...