Hajjin Bana: Alhazzai Za Su Biya Kudin Kujera Miliyan Biyu Da Rabi Daga Ibrahim Ammani Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa, hukumar Aikin Hajji ta ƙasa (NAHCON) Ta fitar da farashin kuɗin kujerar aikin hajji. Hukumar ta bayyana cewar masu son zuwa aikin Hajji na shekarar 2022 a Saudiyya za su biya kusan naira miliyan biyu da rabi kuɗin kujera a hajjin bana. A cewar hukumar, mazauna yankin arewacin Najeriya za su biya jumillar kuɗi naira 2,449,607.89, yayin da na yankin kudu za su biya 2,496,815.29. Mazauna jihohin Borno da Yola kuma za su biya 2,408,197.89, a cewar hukumar.