Ba don ni ba da Buhari bai ci zaɓen 2015 ba - Tinubu

Ba don ni ba da Buhari bai ci zaɓen 2015 ba - Tinubu
  Daga BBC Hausa
Daya daga cikin na kan gaba da ke neman takarar shugabancin Najeriya karkashin jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya ce, shi ne ya zama ja gaba a yaƙin neman zaɓen Shugaba Muhammadu Buhari wanda ya yi nasara a 2015.

Tinubu ya ce shi ne ya bayar da sunan Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin abokin takarar Buhari.

Jaridar Dailay Trust ta ruwaito cewa Tinubu ya bayyana hakan ne a masauƙin shugaban ƙasa a birnin Abeokuta na jihar Ogun, yayin da yake tattaunawa da daliget ɗin APC gabanin zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar.

Yayin ziyarar Bola Tinubu ya samu rakiyar gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu da takwaransa na Kano Umar Ganduje da kuma tsohon Gwamnan Borno Kasim Shettima.

Comments

Popular posts from this blog

In Maiduguri, a 15-year-old girl was killed by a stray bullet from CJTF

The hospital has discharged minors who were victims of viral child abuse videos and they are currently recovering well.

BORNO: In Benishiekh, a man was killed during a tragic dispute over mango farming