Muzgunawa 'yan Najeriya shi ne Burin Gwamnatin Tinubu- Ajaero
Kungiyar Kwadago ta Nijeriya ta caccaki Gwamnatin Bola Tinubu kan karin farashin litar man fetur da aka yi a fadin kasar da ya yi ranar Laraba.
Shugaban NLC na kasa, Kwamared Joe Ajaero ne ya bayyana kaduwar kungiyar cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin wannan Larabar.
Shugaban kungiyar kwafago Kwamared Joe Ajaero.
A cikin sanarwar, Kwamared Ajaero ya ce “da alama dai babu abin da wannan gwamnatin ta sani face kara kudin man fetur ba tare da tuntubar kowa ba, ba kuma tare da an wadata ’yan kasar da hanyoyin rage radadi ba.”
Sanarwar ta ci gaba da cewa tsame hannun dillanci da kamfanin mai na kasa NNPCL ya yi tsakanin ’yan kasuwa da Matatar Dangote abin dubawa ne.
“Ya kamata gwamnati ta sake nazari ta kuma gabatar mana shirin da take yi na bunkasa tattalin arzikin Najeriya, da ci gaban kasa maimakon daukar matakan da ba bu wani tasiri sai dagula lamurra,” in ji NLC.
A ranar Laraba ne aka wayi gari kamfanin NNPCL ya kara farashin man a karo a biyu cikin wata guda.
A birnin Abuja, sabon farashin lita daya ya zama naira 1,030, sabanin yadda ake sayar da shi a baya kan naira 897 a hukumance.
Bayan sabon farashin da NNPCL ya fitar, za a riƙa sayar da duk litar man fetur kan Naira 1,025 a gidajen mansa da ke Kudu maso Yamma sannan a riƙa sayarwa kan Naira 1,045 a Kudu maso Gabashin Nijeriya.
Haka zalika, sabon farashin ya nuna litar man fetur ta koma Naira 1,075 a Kudu maso Kudu da Arewa maso Gabas sannan a riƙa sayarwa kan Naira 1,070 a Arewa maso Yamma da kuma Naira 1,030 a Arewa ta Tsakiya.
Idan za a iya tunawa dai tun a watan Satumba ne kamfanin NNPCL ya ƙara farashin litar man daga N617 zuwa N897 gabanin ya fara sayen man daga Dangote, domin fama da ƙarancin kuɗi a cewar kamfanin na NNPCL.
Comments
Post a Comment