Iniesta ya yi ritaya daga taka leda
Iniesta ya yi ritaya daga kwallo kafa
Andres Iniesta ya sanar da yin ritaya daga taka leda, mai shekara 40 da haihuwa.
Wanda ya taɓa lashe kofin duniya da tawagar Sifaniya, ana cewa ɗaya ne daga cikin waɗanda suka yi fice a fannin tamaula a duniya a tarihi.
Ya taka rawar gani a wasa da yake buga wa daga tsakiya a tawagar Sifaniya da ya yi da Xavi Hernandez da Sergio Busquets da kuma a Barcelona.
Andres Iniesta HOTON: GETTY IMAGES
Ya buga wa Sifaniya wasa 131 da cin ƙwallon da kasar ta lashe kofin duniya a 2010 da ɗaukar kofin nahiyar Turai Euro a 2008 da kuma a 2012.
Iniesta ya yi kaka 22 a Barcelona, wanda ya fara tun daga karamar ƙungiyar da ake kira La Masia academy.
Ya fara buga wa Barcelona tamaula a babbar ƙungiya daga 2002, wanda ya lashe kofi 29 har da La Liga tara da Champions League huɗu daga ciki.
A shekarar 2018 Iniesta ya koma Vissel Kobe ta Japan daga nan ya je Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa a 2023 a ƙungiyar Emirates.
Ya yi na biyu a ƙyautar Ballon d'Or a 2010, yana cikin fitattun ƴan wasa 11 na Fifa karo tara a jere tun daga 2009 zuwa 2017.
Comments
Post a Comment