Fyade: Wani Saurayi Ya jefa Yarinya Cikin Rijiya Bayan Ya yi Mata fyaɗe
Wani saurayi ya shiga hannu kan zargin jefa wata yarinya a rijiya bayan ya yi mata fyaɗe a Kastina
Daga Adamu Aliyu Ngulde, Maiduguri
Wani saurayi ɗan shekara 24 ya shiga hannu kan zargin jefa wata budurwa ’yar shekara 17 a rijiya bayan ya yi mata fyaɗe a Jihar Katsina.
Matashin ya yi wa yarinyar wannan aika-aikra ne bayan ya yi arba da ita a lokacin da mahaifiyar ta aike ta a Rukunin Gidajen Jakadu da ke garin Katsina.
Rundunar ’yan sandan jihar ta ce wanda ake zargin ya yi wa yarinyar barazana ne da wata sharɓe6iyar wuka, inda ya tisa ƙeyarta zuwa wani kango ya yi lalata da ita da ƙarfin tsiya.
Bayan ya kammala kuma a ƙoƙarinsa na ɓatar da sahun abin da ya aikata ne ya jefa ta a cikin wata rijiya sannan ya jefa duwatsu a ciki. Lamarin ya faru ne a ranar 27 ga watan Satumba.
Comments
Post a Comment