Ficewa daga Tampa na jihar Florida shi ne mafi a'ala- Hukumomi
Jama'a da dama na ci gaba da tururwar ficewa daga birnin Tampa na Florida a yayin da mahukunta ke ci gaba da yin gargadin game da barazanar da guguwar Milton ke yi.
Magajin garin, Jane Castor, ya ce duk wanda ya yi kasassaɓar ci gaba da zama, yana iya rasa ransa.
Dogayen layukan ababen hawa sun cunkushe titunan birnin gabanin isowar guguwar a ranar Laraba.
Guguwar na tafiya ne da karfin kadawa da gudun kilomita dari biyu da sittin a cikin sa'a guda, kuma tana nan tafe da ruwa da iska.
ASALIN HOTON, KATHIE ALLEN-TIERNEY
A yanzu dai ta yada zango ne a yankin Yucatan na Mexico, inda tuni aka rufe makarantu a yankin tare da dakatar da zirga-zirgar jama'a.
A watan da ya gabata ne guguwar Helene ta ratsa yankunan kudu maso gabashin Amurka, inda ta kashe mutane sama da dari biyu.
Madogara: BBC
Comments
Post a Comment